Blog

  • Sauye-sauye 6 da aka samu tun bayan zaɓen Tinubu a 2023

    Sauye-sauye 6 da aka samu tun bayan zaɓen Tinubu a 2023

    Ƴan Najeriya na shirin sake komawa rumfunan zaɓe a watan Janairun 2027, inda miliyoyin masu kaɗa ƙuri’a za su zaɓi shugaban ƙasa, gwamnoni, da kuma ƴan majalisun tarayya da na jihohi.

    A zaɓen 2023, mutane da dama sun sa ran cewa amfani da sabbin fasahohi a zaɓe, yawan fitowar matasa kaɗa ƙuri’a da kuma zazzafar takara tsakanin manyan ƴan takara uku za su ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya.

    Sai dai matsalolin da aka samu daga hukumar zaɓe ta INEC na rashin nuna sakamakon zaɓe ta intanet (IReV) sun haifar da shakku kan sahihancin zaɓen a idanun mutane da dama.

    An ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar. Sai dai manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, sun ƙalubalanci sakamakon a kotu, amma Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Tinubu.

    Bayan shafe shekaru uku, an ga sauye-sauye dama a fagen siyasa da tattalin arziki Najeriyar. An samu sauye-sauyen dokokin zaɓe, jam’iyyar APC ta ƙara faɗaɗa tasirinta a siyasance, yayin da ƴan ƙasar ke ci gaba da ƙorafi kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da matsalar wutar lantarki.

  • Yadda ƴansanda suka tilasta wa shugaban yaƙi da rashawa na Najeriya bayar da cin hanci

    Yadda ƴansanda suka tilasta wa shugaban yaƙi da rashawa na Najeriya bayar da cin hanci

    Wani abu mai kama da almara ko? Amma da gaske ne ya faru.

    An daɗe ƴan Najeriya na kokawa game da ƙazancewar ayyukan rashawa a ma’aikatu da hukumomin gwamnati, kuma hukumar ƴansanda ta ƙasar na cikin waɗanda a kodayaushe ake nunawa, kan cewa jami’anta na yawan karɓar kuɗi daga al’umma sa’ilin da suke bakin aiki.

    Amma an ce kwana dubu ta ɓarawo, kwana ɗaya kuma ta mai kaya.

    A wannan karo shugaban hukumar yaƙi da rashawa da laifuka makamantan haka ICPC na Najeriya, Musa Aliyu ne ya faɗa hannun wasu jami’an ƴansanda a birnin Abuja, waɗanda suka buƙace shi ya ba su kuɗi bayan zargin shi da laifin karya doka.

    Tuni hukumar ƴansanda ta tabbatar da faruwar lamarin har ma ta bayyana cewa ta fara ɗaukar matakin kan lamarin.

  • Chelsea, Arsenal da Spurs na zawarcin Rashford, Arsenal na son Konsa

    Chelsea, Arsenal da Spurs na zawarcin Rashford, Arsenal na son Konsa

    Tottenham, da Chelsea da Arsenal na zawarcin ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford, sai dai United din ba ta son siyar da shi ga wata ƙungiya da ke Ingila. (The I – subscription required)

    Mai tsaron ragar Aston Villa da Arjantina Emiliano Martinez, 33, ya kasnace mai tsaron ragar da Juventus ke hari, yayin da Arsenal ke son ɗauko ɗan wasan Aston Villar da Ingila Ezri Konsa. (Telegraph – subscription required)

    Nottingham Forest sun shiga mataki na gaba kan tattaunawa da ɗan wasan Sporting CP da Ivory Coast Ousmane Diomande, 22. (Fabrizio Romano)

    Juventus na son ɗauko ɗan wasan West Ham’s da Fransa Jean-Clair Todibo. (Gazzetta dello Sport – in Italian)

    Manchester United na kan aniyar ta na ɗauko sabon dan wasan tsakiya, sai dai sun sassauta kan son siyen ɗan wasan Brighton da Kamaru Carlos Baleba da dan wasan Bournemouth Guernseyman Alex Scott, saboda tsadar farashin da suka sa musu. (Teamtalk)

  • DSS Ta Biya Wani Mutumi Diyyar N3m Bayan Kuskuren Kama Shi Kan Zargin Ta’addanci

    DSS Ta Biya Wani Mutumi Diyyar N3m Bayan Kuskuren Kama Shi Kan Zargin Ta’addanci

    DSS ta kuma sake nazarin tuhume-tuhume fiye da 30, tare da biyan diyyar sama da naira miliyan 300 ga mutanen da aka tsare ba bisa…

    Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta saki wani manomi ɗan asalin Jihar Kaduna, tare da wanke shi daga zargin alaƙa da ƙungiyar Boko Haram, sannan ta biya shi diyyar naira miliyan uku.

    Shugaban hukumar DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ne ya bayar da umarnin sakin mutumin, Nura Idris, wanda manomi ne kuma makiyayi daga Ƙaramar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna, yayin da ake ci gaba da nazarin batutuwan waɗanda aka tsare ba bisa ƙa’ida ba.

    Majiyoyin tsaro sun ce binciken cikin gida da DSS ta gudanar ya tabbatar da cewa babu wata alaƙa tsakanin Nura da mayaƙan Boko Haram.

    Majiyoyin sun ce wata hukumar tsaro ce ta kama Nura a watan Yunin 2024 a garin Suleja da ke Jihar Neja, kafin daga bisani ta miƙa shi ga DSS bisa zargin yana da alaƙa da ta’addanci.

  • Tarnaƙin Da Argentina Da Sifaniya Suka Ratsa Zuwa Wasan Ƙarshe Na Gasar Kofin Duniya

    Tarnaƙin Da Argentina Da Sifaniya Suka Ratsa Zuwa Wasan Ƙarshe Na Gasar Kofin Duniya

    Wasan Argentina da Ingila na ɗaya daga cikin manyan wasannin da aka yi ɗokin gani.

    A ranar Talatar makon nan ce abin da masu iya magana kan ce “ba a sanin maci tuwo sai miya ta ƙare” ya tabbata a kan tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa yayin da ta yi bankwana da Gasar Kofin Duniya ta 2026.

    Lamarin na zuwa ne bayan tawagar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta taka mata burki, yayin da doke ta da ci 2-0 a wasan kusa da na ƙarshe da suka fafata, duk da cewa Les Bleus ta kasance cikin tawagogin da suka fi ƙayatar da masu kallo tun farkon soma gasar.

    Faransa dai tana sahun gaba cikin rukunin ƙasashen da aka yi hasashen za su lashe babbar gasar tamaular ta duniya, amma sai ga shi Sifaniya ta yi tumu-tumu da ita duk da irin zaƙaƙuran ’yan wasa da ta tara da har ake ganin ba ta da wani naƙasu a kowace lamba.

    Tawagar wadda Didier Deschamps ke jagoranta ta zura ƙwallaye 16 a wasanni shida kafin karawar, amma ta kasa nuna irin wannan bajinta a yayin karawa da Sifaniya.

    Sifaniya dai ta bai wa Faransa mamaki wadda take cike da dabaru na tsaron baya da kuma tsakiya irinsu Rodri da Dani Olmo da Fabian Ruiz, abin da ya hana zaƙaƙuran ’yan wasan Faransa taka rawar gaban hantsi.

    Ƙwazon tsaron bayan tawagar Sifaniya ƙarƙashin jagorancin Luis de la Fuente ya kashe kaifin harin taurarin ’yan wasan Faransa a fafatawar.

    An samu nasarar saka ƙwallon farko a raga ne a minti na 22 bayan da Lucas Digne ya yi wa shahararren matashin ɗan wasa Lamine Yamal ƙeta a cikin da’ira ta 18, kuma alƙalin wasa ya bayar da bugun fenariti, wanda Mikel Oyarzabal ya buga cikin natsuwa kuma ƙwallon ta wuce mai tsaron raga Mike Maignan.

  • Sauye-Sauyen Da Majalisar Tarayya Ta Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Na 1999

    Sauye-Sauyen Da Majalisar Tarayya Ta Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Na 1999

    ’Yan majalisa sun kada kuri’ar amincewa da wasu dokoki yayin da suka yi watsi da wasu.a

    A ranar Talata ’yan Majalisar Dokokin Tarayya da suka hada na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai suka fara kada kuri’a kan sauye-sauye 68 da aka gabatar na yi wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima.

    A zaman wanda Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa, Dolapo Osinbajo da Ministar Harkokin Mata, Paulen Talen suka halarta, ’yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da wasu dokoki yayin da suka yi watsi da wasu.

    Aminiya ta rairayo wasu daga cikin sauyen-sauyen da suka samu shiga Kundin Tsarin Mulkin da wadanda suka yi bandaro bayan ’yan majalisar sun kada kuri’ar kin amincewa da su kamar haka:

    1. Majalisar Wakilai ta amince da kudirin wajabta wa yara samun ilimi kyauta. Hakazalika ilmi ya zama hakki na dukkan dan Najeriya.
    2. Majalisar Dattawa ta ki amincewa da kudirin kirkiro wa mata kujeru na musamman.
    3. Majalisar Wakilai ta ki amincewa da biyan fansho har zuwa lokacin mutuwa ga Shugabannin Majalisa.
    4. Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudirin halasta zaman sauraron shari’a daga nesa ta hanyar bidiyo ko makamancin haka.
    5. Majalisar Wakilai ta amince da kudirin wajabta wa Shugaban kasa nada dan asalin Babban Birnin Kasar na Abuja a matsayin Ministan Abuja. Ta kuma amince da kudirin samar da Ofishin Magajin Garin Abuja.
    6. Majalisar Wakilai ta yi watsi da bukatar bai wa ’yan Najeriya mazauna ketare damar kada kuri’a a lokutan zabukan dake gudana a nan gida Najeriya.
    7. Majalisar Dattawa ta amince da kudirin bai wa Majalisa ikon umartar Shugaban Kasa ko Gwamna ya bayyana a gabanta.
    8. Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudirin sanya wa Shugabannin Majalisa da na Hukumomin Shari’a rigar kariya kamar yadda take a kan Shugaban Kasa da Gwamnoni.
    9. Majalisun biyu sun amince da kudirin bai wa Majalisun Dokoki na Jiha da Kananan Hukumomi da Hukumomin Shari’a yancin cin gashin kansu a kan duk wata harkalla ta kudi.
    10. Majalisar Wakilai ta yi watsi da dokar da za ta bai wa majalisa damar zagaye Shugaban Kasa tare da yin gaban kanta idan ya ki amincewa da wata dok
  • Majalisa Ta Buƙaci A Bi Diddigin Duk Kadarorin Da Ake Ƙwacewa Tun Daga 1999

    Majalisa Ta Buƙaci A Bi Diddigin Duk Kadarorin Da Ake Ƙwacewa Tun Daga 1999

    Ƙudirin ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike da tantance dukkan kadarorin da aka ƙwace.

    Yan Majalisar Wakilai sun ba da umarnin gudanar da bincike kan dukkan kadarorin da aka ƙwace a cikin gida ko waɗanda aka ƙwato aka dawo da su daga ƙetare tun bayan dawowar Najeriya kan mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999 zuwa yanzu.

    Majalisar ta ce akwai damuwa kan rashin gaskiya da rashin kiyaye ka’idojin gudanarwa da kuma matsalolin adana bayanai.

    Matakin ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Arochukwu/Ohafia ta Jihar Abia, Ibe Okwara Osonwa, ya gabatar.

    about:blank Ƙudirin ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike da tantance dukkan kadarorin da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da hukumomin tsaro da ma’aikatu, da hukumomi da cibiyoyin gwamnati haɗe da hukumomin sa ido da kuma kotuna ke kula da su.