Tottenham, da Chelsea da Arsenal na zawarcin ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford, sai dai United din ba ta son siyar da shi ga wata ƙungiya da ke Ingila. (The I – subscription required)
Mai tsaron ragar Aston Villa da Arjantina Emiliano Martinez, 33, ya kasnace mai tsaron ragar da Juventus ke hari, yayin da Arsenal ke son ɗauko ɗan wasan Aston Villar da Ingila Ezri Konsa. (Telegraph – subscription required)
Nottingham Forest sun shiga mataki na gaba kan tattaunawa da ɗan wasan Sporting CP da Ivory Coast Ousmane Diomande, 22. (Fabrizio Romano)
Juventus na son ɗauko ɗan wasan West Ham’s da Fransa Jean-Clair Todibo. (Gazzetta dello Sport – in Italian)
Manchester United na kan aniyar ta na ɗauko sabon dan wasan tsakiya, sai dai sun sassauta kan son siyen ɗan wasan Brighton da Kamaru Carlos Baleba da dan wasan Bournemouth Guernseyman Alex Scott, saboda tsadar farashin da suka sa musu. (Teamtalk)
