DSS Ta Biya Wani Mutumi Diyyar N3m Bayan Kuskuren Kama Shi Kan Zargin Ta’addanci

DSS ta kuma sake nazarin tuhume-tuhume fiye da 30, tare da biyan diyyar sama da naira miliyan 300 ga mutanen da aka tsare ba bisa…

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta saki wani manomi ɗan asalin Jihar Kaduna, tare da wanke shi daga zargin alaƙa da ƙungiyar Boko Haram, sannan ta biya shi diyyar naira miliyan uku.

Shugaban hukumar DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ne ya bayar da umarnin sakin mutumin, Nura Idris, wanda manomi ne kuma makiyayi daga Ƙaramar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna, yayin da ake ci gaba da nazarin batutuwan waɗanda aka tsare ba bisa ƙa’ida ba.

Majiyoyin tsaro sun ce binciken cikin gida da DSS ta gudanar ya tabbatar da cewa babu wata alaƙa tsakanin Nura da mayaƙan Boko Haram.

Majiyoyin sun ce wata hukumar tsaro ce ta kama Nura a watan Yunin 2024 a garin Suleja da ke Jihar Neja, kafin daga bisani ta miƙa shi ga DSS bisa zargin yana da alaƙa da ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *