Gwamnatin Jigawa za ta ci gaba da samar da cibiyoyin koyar da matasa fasahar sadarwa (ICT)

Daga Wakilinmu

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana aniyarta na ci gaba da samar da cibiyoyin koyar da matasa ilimin fasahar sadarwa ta zamani, wato ICT, domin tunkarar ƙalubalen zamani.

Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamar da sabuwar cibiyar ICT a makarantar sakandaren ’yan mata ta gwamnati, Famfo Goma, da ke Hadejia, wadda Hajiya Safiya Idris Kallamu ta samar.

Gwamnan, wanda Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Zamani da Tattalin Arziki ta Jihar Jigawa, Dr Mohammed Hassan, ya wakilta, ya buƙaci mahukuntan makarantar da ɗalibai su yi amfani da cibiyar yadda ya kamata domin cimma manufar samar da ita.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje, ya bayyana farin cikinsa bisa samar da cibiyar, tare da kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan kyakkyawan aiki wajen tallafa wa ci gaban matasa.

A nata jawabin, Hajiya Safiya Idris Kallamu ta ce an samar da cibiyar ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa da Sa-Ido kan Abubuwan da Ƙasa ke Samarwa, wato National Content Development and Monitoring Board, domin inganta rayuwar al’umma, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

Tun da farko, Shugabar Makarantar, Hajiya Habiba Ahmed Baffa, ta bayyana wasu nasarorin da makarantar ta samu, waɗanda suka haɗa da zagaye makarantar da katanga, ƙarin ajujuwa, samar da kayan karatu da inganta harkokin koyarwa da koyo.

Ta kuma gode wa dukkan waɗanda suka halarci bikin ƙaddamar da cibiyar, wadda za ta bai wa ɗalibai 100 damar samun horo kan amfani da kwamfuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *