Daga Abubakar Rabilu Gombe
Majalisar Masarautar Arewarmu Duniyarmu African Chiefdom and Council ta naɗa Dakta Suraj AbdulKarim Kwami a matsayin Sarkin Lafiyar Arewa, a wani mataki na karrama gudunmawarsa da kuma ƙarfafa rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen bunƙasa al’umma.
Da yake jawabi a wajen bikin, shugaban majalisar, Mai Martaba Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, ya ce an zaɓi waɗanda aka naɗa ne bisa la’akari da gudunmawarsu ga al’umma, kishin jama’a da jajircewarsu wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai.
Ya bayyana cewa majalisar ta ɗauki matakin ne domin amfani da sarautun gargajiya wajen haɗa kan al’ummomin Afirka, tare da ƙarfafa dangantaka tsakanin sarakuna, malamai, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, sarautun da aka bayar ba wai don ado ko ɗaukaka sunayen waɗanda aka naɗa ba ne, illa wata babbar amana ce da ke buƙatar sadaukarwa da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima.
“Wannan sarauta ba ado ba ce kawai, babbar amana ce da nauyi a wuyansu. Muna son su zama jakadun alheri, zaman lafiya da haɗin kai a duk inda suke a nahiyar Afirka,” in ji shi.
Ambasada Haruna ya buƙaci sabbin masu sarautun da su yi amfani da matsayinsu wajen sasanta rikice-rikice, taimaka wa marasa ƙarfi, ƙarfafa zumunci da kuma kare martabar al’adu da addinan al’ummomin Afirka.
Ya ƙara da cewa manufar majalisar ita ce gina Afirka mai haɗin kai da fahimtar juna, ba tare da nuna bambanci tsakanin ƙabila, addini ko ƙasa ba.
Da yake nuna godiyarsa bayan karɓar sarautar, Dakta Suraj AbdulKarim Kwami ya bayyana farin cikinsa bisa karramawar da majalisar ta yi masa, tare da gode wa shugabanninta bisa amincewa da suka nuna masa.
Sabon Sarkin Lafiyar Arewa ya yi alƙawarin yin amfani da sabon matsayinsa wajen ƙarfafa haɗin kai, inganta fahimtar juna da kuma bunƙasa zaman lafiya tsakanin al’ummomi.
Ya ce zai yi ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora masa yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa sarautar ta zama wata hanya ta ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin al’ummomin Afirka, ba tare da nuna bambanci ba.
