Gwamnatin Tarayya ta ware naira biliyan 2 domin tallafawa sabon shirin noman alkama

Daga Wakilinmu

Gwamnatin Tarayya ta ware kuɗi har Naira Biliyan Biyu (N2b) domin tallafa wa sabon shirin noman alkama a wani mataki na ƙara inganta wadatar abinci da samar da guraben ayyukan yi ga al’umma.

Ko’odinetan Ƙungiyar Manoman Alkama da sarrafata ta Ƙasa na shiyyar Arewa maso Yamma, Injiniya Tasiu Ahmed ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai fadar Sarkin Hadejia inda ya miƙa masa takardar shaidar naɗa shi a matsayin Uban Ƙungiyar na Ƙasa.

Injiniya Ahmed ya bayyana cewa shirin na da burin Noma Alkama a faɗin kadada 250, inda za a fara da kadada Bakwai (7) a matsayin gwaji daga ciki za a Noma kadada Biyar (5) a Jihar Jigawa, yayin da sauran kadada Biyu (2) za a raba tsakanin jihohin Kaduna, Sokoto da Zamfara.

Ya ce tuni masana suka gudanar da bincike tare da tantance wuraren da suka dace, inda suka zaɓi yankin Masarautar Hadejia da ke Jihar Jigawa domin aiwatar da shirin daga nan kuma ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su bayar da goyon bayan da ya dace don cimma muradun shirin.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji Dakta Adamu Abubakar Maje ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa wannan shiri tare da ba da shawarar amfani da ingantattun nau’ikan irin Alkama da zasu dace da yanayin yankin domin tabbatar da ɗorewar shirin.

Sarkin ya kuma nuna farin cikin sa bisa naɗa shi a matsayin Uban Ƙungiyar na Ƙasa, tare da alƙawarin bayar da cikakken goyon baya domin bunƙasa ayyukan ƙungiyar.

#MGT

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *