Karamar Hukumar Guri ta na kashe sama da Naira miliyan sha daya wajen tallafa wa al’umma a sassa daban-daban

Daga Wakilinmu

Majalisar Ƙaramar Hukumar Guri ta bayyana cewa tana kashe kuɗi sama da naira Miliyan Goma sha Ɗaya (N11m) a duk wata wajen tallafa wa al’umma a sassa daban-daban na ƙaramar hukumar.

Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Abubakar Umar Dan Barde, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da jami’in yaɗa labaran ƙaramar hukumar, a wani ɓangare na bikin cika shekaru biyu da hawansa mulki, domin bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Ya bayyana cewa wannan kuɗi bai haɗa da tallafin da ake bayarwa lokaci zuwa lokaci ba, kamar tallafin Ɗalibai, taimakon marasa lafiya, jari ga masu ƙananan sana’o’i da sauran nau’o’in tallafi.

Alhaji Abubakar Dan Barde ya ce majalisar ta yi koyi da shirye-shiryen samar da ayyukan yi na gwamnatin jihar Jigawa, inda ta ɗauki matasa da suka kammala karatun su 300 aiki ƙarƙashin shirye-shiryen G-Teach da G-Health, tare da ware musu naira miliyan tara (N9m) a duk wata.

Ya ƙara da cewa majalisar tana ware naira miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin (N1.250m) a duk wata domin tallafa wa ma’aikatan da suka yi ritaya, waɗanda yawansu ya kai 250, haka kuma ta ɗauki matasa 11 a matsayin masu rajistar takardun shaidar haihuwa ta hanyar intanet, suna karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari uku da hamsin (N350,000) a kowanne wata.

Haka zalika, Majalisar ta ɗauki matasa 11 domin taimakawa wajen aiwatar da shirin JICHMA na Gwamnatin jiha, inda take ware musu naira dubu dari da goma (N110,000) a kowanne wata.

Bugu da ƙari Shugaban yace an ɗauki ma’aikata 20 na wucin gadi a cibiyoyin kiwon lafiya na yankin inda suke karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida (N600,000) a duk wata, domin tallafa wa harkokin kiwon lafiya da samar wa matasa ayyukan yi.

A ƙarshe, Alhaji Dan Barde ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar ta Guri da su ci gaba da mara wa shirye-shiryen gwamnati baya domin cimma manufofin inganta rayuwar al’umma da bunƙasa ci gaban yankin don ɗorewar ƙudirin.

#MGT

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *