Daga Hussaini Yero
Dan Takarar Sanatan Zamfara Ta Arewa, Sani Abdullahi Shinkafi ya kalubalanci zaben. kuma tare rantse da Alkur’ani mai tsaki cewa, ba’ayi zabenba.
Zaben fidda gwani da aka gudanar a Ranar Litinin 2/11/2026, Shinkafi
ya kuma yi kira ga wadanda suka gabatar da sakamakon zaben da su fito bainar jama’a kamar yadda yayi su dauki Alkur’ani mai tsaki su rantse da shi .
Shinkafi ya bayyana rantsuwar ne a taron magoya bayansa da yayi a Taula hotal da ke Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara.
Dan Takarar Sanata Sani Shinkafi, yayi kira ga Dakta Auwal Aliyu da ya bayyana samun nasarar Sanata Sahabi Yau a zaben, ya bayyana gaban jama’a ya rantse da Alkur’ani cewa, an yi zabe a runfunan zabe da muke dasu a Zamfara Ta Arewa.Haka Shima Wanda ya ayyukan nasarar Zaben Sanata Tijani Yahaya Kaura,Sani Abdullahi ,Shima ya bayyana gaban jama’a ya rantse da Alkur’ani mai tsaki akan cewa, an yi zabe ko ina a Zamfara Ta Arewa.
Shinkafi ya tabbatar da cewa, babu inda aka yi zabe wasu ne suka rubuta samakon zaben suka bayyana wa magoya bayansu, “akan haka na ke tabbatar wa mutanan Zamfara ta Arewa cewa, zai garzaya kotu dan neman hakkina akan wannnan, zabe ga uwar jam’iyya APC ta kasa”. In ji Shinkafi.
Shinkafi yayi kira ga Gwamna Dauda Lawal da Sanata Abdul’aziz Yari Abubukar Da karamin Minista Matawalle akan su fidda hannayesu cikin wannnan magudin zaben ko yayi masu illa a zaben shekara ta 2027.
