Zaben 2027 : Hasashe Na Nuni Da Cewa Tinubu, Sanata Yari, Gwamna Dauda Na Iya Rasa Jihar Zamfara

Ra’ayi : Daga Farfesa Abubakar Ahmad Abdullahi, Manazarcin Siyasa

Siyasa mugun wasa, duk jam’iyyar da ta rasa masu tara mata jama’a a ƙasa, ta rasa ƙarfin cin zaɓe.

A kan wannan ne nake jawo hankalin ‘yan Najeriya kan murabus mai tayar da hankali da ‘yan majalisar dokokin Jihar Zamfara takwas masu ci suka yi daga jam’iyyar APC ranar Asabar, 3/10/2026.

A wasiku daban-daban zuwa ga shugabannin mazabunsu, ‘yan majalisar sun sanar da ficewarsu daga jam’iyya mai mulki jam’iyyar da ta hannunta suka yi ƙaƙƙarfan hamayya da Gwamna Dauda Lawal lokacin yana PDP.

Wannan babban abun kunya ne ga shugabancin APC a Zamfara, musamman Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu da Shettima.

Gwamna Dauda Lawal ya kamata ya ɗauki babban laifi. Lokacin da rikici ya ɓarke a Majalisar Dokokin Jihar, a matsayinsa na shugaba ya kamata ya yi kira da a kwantar da hankali. Sai dai ya ƙara rura wuta don amfanin kansa. ‘Yan majalisar sun zarge shi da cin zarafin ofisdin su, amma ya ƙi Yardar da ayi sulhu.

Ko bayan sauya sheƙa daga PDP zuwa APC – wanda da yawa suka gani a matsayin ƙoƙarin tabbatar da wa’adi na biyu – ya ƙi warware rikicin Majalisa.

An dakatar da ‘yan majalisar takwas ne a 27 ga Fabrairu 2024 Karkashin shugabancin kakakain Majalisar Bilyaminu Moriki bisa zargin karya Order 10, Rule 9. Sun musanta, suna cewa an hukunta su ne saboda sun ɗaga murya kan matsalar tsaro a yankunansu. Sun shafe watanni 31 da dakatarwa ba tare da albashi ba.

Dattawa irin su Janar Aliyu Mohammed Gusau, Majalisar Ulama ta Zamfara, tsohon Mataimakin Gwamna Ibrahim Wakkala Muhammad, da Hon. Kabiru Ibrahim Masari sun yi sulhu, amma Gwamnan ya ƙi.

Mafi muni a Zamfara ta Yamma, yankin Yari, inda biyar daga cikin takwas suka fito, ciki har da Hon. Aliyu Ango Kagara na Talata Mafara ta Kudu – ƙaramar hukumar Yari da kanta.

Sauran sun haɗa da Hon. Ibrahim T. Tukur na Bakura, Hon. Faruk Musa Dosara na Maradun I, Hon. Bashir Abubakar Masama na Bukkuyum ta Arewa, Hon. Bashar Aliyu Gummi na Gummi I, Hon. Nasiru Abdullahi Maru na Maru ta Arewa, Hon. Basiru Bello na Bungudu ta Yamma, da Hon. Mukhtar Nasiru na Kaura Namoda ta Arewa.

Wannan babbar barazanace A 2027 ga Sanata Yari, ‘yan majalisar tarayya da sanata na Zamfara ta Tsakiya da ta Arewa, da Gwamna Lawal da kansa.

Babbar matsalar ita ce yaƙi tsakanin sansanin Yari da na Matawalle, na Canjin gida -ghda Shima babbar barazanace a Zaben 2027.

Sauran waɗanda abin ya shafa sun haɗa da tsohon Gwamna Ahmad Sani Yariman Bakura (Hon. Ibrahim T. Tukur – Bakura), Ministan Ƙasa na Tsaro Dr. Bello Matawalle (Hon. Faruk Musa Dosara – Maradun I), Mataimakin Gwamna Mani Malam Mumuni (Hon. Bashir Abubakar Masama – Bukkuyum ta Arewa), da Shugaban Kwamitin Dattawan APC Alhaji Salihu Maibuhu Gummi (Hon. Bashar Aliyu Gummi – Gummi I).

A Zamfara ta Tsakiya: Hon. Nasiru Abdullahi Maru (Maru ta Arewa) da Hon. Basiru Bello (Bungudu ta Yamma) sun yi murabus. A Zamfara ta Arewa: Hon. Mukhtar Nasiru (Kaura Namoda ta Arewa) ya yi murabus.

Akan haka na ke kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta kirawo Matawalle, Yari da Gwamna Lawal zuwa tattaunawa domin sake tsara APC a Zamfara. Rashin hakan zai jawo mummunar faɗuwa ga Tinubu A Zamfara A 2027

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *