ADC Ta Yi Alkawarin Dawo da Tallafin Man Fetur, Magance Matsin Rayuwa da Rashin Tsaro….Sanata Nakudu

Daga Mati Ali

Dan takarar gwamnan Jihar Jigawa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Sanata Sabo Mohammed Nakudu ya bayyana cewa jam’iyyar ta himmatu wajen magance matsin tattalin arziki da rashin tsaro ta hanyar dawo da tallafin man fetur.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Nakudu ya danganta matsin rayuwar da ’yan Najeriya ke fuskanta da cire tallafin man fetur da aka sanar a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Ya ce rage farashin man fetur na tsawon wata guda da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sanar, biyo bayan shawarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya gabatar, ya nuna aniyar jam’iyyar ADC na dawo da tallafin domin rage wa ’yan ƙasa nauyin tsadar rayuwa.

Nakudu ya ce manufar ADC ita ce ceto ’yan Najeriya daga matsin tattalin arziki da rashin tsaro, waɗanda ya danganta matsalolin da Kasa ta shiga abisa manufofin jam’iyyar APC mai mulki.

Ya ƙara da cewa dawo da tallafin man fetur na daga cikin matakan da jam’iyyar ke shirin ɗauka domin rage matsalolin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *