Nakudu Project 2027 Ya Horar da Matasa 300 Kan Dabarun Yaɗa Saƙonnin ADC a Kafafen Sadarwa a Jigawa

Daga Mati Ali

Shirin Project Nakudu 2027 ya kammala horo na matakai uku kan dabarun yaɗa labarai da sadarwa ta zamani ga masu fafutukar yaɗa saƙonnin jam’iyyar ADC a kafafen sada zumunta a Jihar Jigawa, inda kusan mutum 300 daga ƙananan hukumomi 27 suka amfana.

An gudanar da kashi na ƙarshe na horon a ranar Asabar a garin Gumel, tare da mahalarta daga ƙananan hukumomi 12 na Mazabar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma, domin ƙarfafa yaɗa manufofin jam’iyya ta kafafen zamani, daidaita saƙonnin yaƙin neman zaɓe da bunƙasa wayar da kan al’umma tun daga tushe gabanin zaɓen 2027.

Mai gudanar da shirin, Alhaji Mohammed Sabo Nakudu, ya ce an ƙaddamar da horon ne domin ƙarfafa tsarin sadarwa da yaƙin neman zaɓen ADC ta kafafen sada Zumunta na zamani.

Ya buƙaci mahalarta su kasance masu ladabi, jajircewa, himma da sanya ido, yana mai jaddada muhimmiyar rawar da matasa za su taka wajen kare ƙuri’un ADC, tun daga rumfunan zaɓe har zuwa kammala dukkan matakan zaɓe.

A cikin wata lacca, Hon. Ahmed Rufai Gumel, tsohon shugaban ƙungiyar yaɗa saƙonnin APC ta kafafen sada zumunta a Jihar Jigawa kuma ɗan takarar ADC na Majalisar Dokokin Jihar, ya jaddada muhimmancin kiyaye daidaiton saƙonnin siyasa, haɗin kai wajen gudanar da ayyukan yaɗa saƙonni a intanet, da tallata dukkan ’yan takarar ADC.

Manyan jiga-jigan ADC da suka halarci taron sun buƙaci mahalarta su riƙa yaɗa sahihan bayanai, yaƙi da labaran ƙarya, tare da gabatar da manufofi da shirye-shiryen jam’iyyar cikin ƙwarewa da ɗaukar nauyi.

Shirin horon mai matakai uku ya shafi dukkan mazabun sanatoci uku na Jihar Jigawa, da nufin gina rundunar masu yaɗa saƙonnin siyasa ta kafafen zamani mai haɗin kai, gabanin babban zaɓen 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *