Daga Wakilinmu
Sanata Abdul Ningi ya bayyana yadda tsohon abokin aikinsa, Sanata Bello Mandiya, ya rasu bayan zargin zamewa da ya yi a banɗaki har ya bugi kansa, lamarin da ya sa ya fadi a mace a gidansa da ke Abuja ba tare da an san halin da yake ciki ba har tsawon sa’o’i 72.
Sanata Ningi, wanda ke wakiltar mazabar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar, inda ya nuna alhininsa kan rasuwar marigayin.
A cewar Ningi, an gano gawar Mandiya ne a ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, bayan maƙwabta sun fara jin wani wari yana fitowa daga gidansa.
Ya ce wani babban limamin masallacin Apo ma ya nuna damuwa bayan lura da cewa Mandiya, wanda ya saba halartar sallolin farilla guda biyar, bai bayyana a masallaci ba har tsawon kwanaki uku a jere.
Ningi ya bayyana cewa Mandiya ya shirya fita domin halartar sallar Juma’a a ranar 4 ga Satumba, 2026, bayan wani abokin aikinsa ya gan shi da ƙarfe 11 na safe.
Sai dai, bayan ya dawo gidansa, wanda yake zaune shi kaɗai, an ce ya shiga banɗaki domin yin wanka, amma bayan ya fito sai ya zame ya bugi kansa.
Ningi ya ce marigayin ya ajiye hularsa da wayoyinsa a kan gado kafin ya shiga banɗakin, amma babu wanda ya san abin da ya faru da shi.
