Dr. Ismaila Yusuf: Mutumin Kirki, Mai Amfani da Damarsa Wajen Hidimtawa Al’umma

Dr. Ismaila Yusuf

Daga Muhd Ishaq Sambo Hadejia

Wasu mutane ba sa samun daraja da kima saboda mukaman da suke riƙe da su kawai, a’a, suna samun wannan matsayi ne saboda kyawawan halayensu, tawali’u da kuma irin tasirin alherin da suke yi ga mutanen da ke kewaye da su. Dr. Ismaila Yusuf yana daga cikin irin waɗannan ’ya’ya nagari kuma fitattu.

Dr. Ismaila Yusuf, ɗan asalin Kaugama kuma abin alfahari ga Masarautar Hadejia, ya yi fice ta fuskar ilimi, jajircewa, ƙwarewa da kuma sadaukar da kai wajen gudanar da hidimar jama’a. A matsayinsa na ma’aikacin gwamnati a Ma’aikatar Kananan Hukumomi da ci gaban al’umma ta Jihar Jigawa, yana wakiltar nagartattun halaye na riƙon amana, ƙwarewa da kishin ci gaban al’umma tun daga tushe.

Abin da ya ƙara sanya shi abin ƙauna da girmamawa shi ne irin tawali’u da sauƙin kai da yake da shi. Yanayinsa na son jama’a, ladabi, mutuntawa da kuma murmushinsa na dabi’a sun sanya shi zama mutum mai sauƙin mu’amala da kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Ya fahimci cewa hidimar jama’a a haƙiƙanin gaskiya hidima ce ga mutane, al’umma da kuma ƙoƙarin kyautata rayuwarsu.
Babban matsayinsa na ilimi, wanda ya haɗa da digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanar da Harkokin Jama’a, shaida ce ta irin yadda yake ba ilimi muhimmanci. Haka kuma, ƙwarewarsa ta aiki na nuni irin jajircewarsa wajen inganta tsarin gudanar da ƙananan hukumomi, tabbatar da riƙon amana, bunƙasa ma’aikata da kuma ƙarfafa kyakkyawan shugabanci a matakin ƙasa da al’umma.

Dr. Ismaila ba mutum ba ne wanda hangen nesansa ya tsaya ga garinsa ko al’ummarsa kawai. zuciyarsa tana tare da Jihar Jigawa baki ɗaya. Daga Kaugama zuwa Hadejia, daga wannan ƙaramar hukuma zuwa waccan, irin gudunmawarsa da kyakkyawar mu’amalarsa sun cancanci yabo da girmamawa.

Kaugama na da dalilin yin alfahari da shi. Masarautar Hadejia na da dalilin yin murnar kasancewarsa ɗanta. Jihar Jigawa na da dalilin yaba masa da kuma jin daɗin irin gudunmawarsa.

A matsayinsa na ƙwararren masanin aiiki, ya kasance mutum mai himma da jajircewa, mai tawali’u, bawan jama’a, kuma mutum ne da yake tafiya da kowa tare da shi.

Allah Ya ci gaba da bai wa Dr. Ismaila Yusuf hikima, basira, ƙarfi da lafiya, Ya kuma buɗe masa ƙofofin ƙarin dama domin ya ci gaba da yi wa bil’adama hidima da kuma bayar da tasa gudunmawar wajen ci gaban Jihar Jigawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *