Rayuwa Da Tasiri Na Marigayi Alhaji Ladan Wapa

Daga Husain Kabir Yar’adua

A cikin mutanen da na samu damar sanin su a rayuwata, akwai Marigayi Alhaji Ladan Wapa yana daga cikin mutanen da suka bar mani babban tarihi na alheri, tausayi da taimakon al’umma.

Ina zaune a Filin Samji, gidan Marigayin kuma yana Kofar Durbi. Na kasance ina ganin irin yadda yake mu’amala da mutane da kuma irin gudummawar da yake bayarwa ga al’umma.

Marigayi Alhaji Ladan Wapa yana halartar wasu darussa da Malaminmu Dr. Zakariya Aliyu Sandamu ya kasance yana gabatarwa duk ranar Asabar da Lahadi da asuba a Masallacin Alhaji Ali KD. Abin da nake lura da shi shine, kusan duk lokacin da ya halarta, sai ya yi tambaya ko ya kara wani bayani a kan abin da Malamin ya gabatar.

Har ana cewa idan aka je darasi aka ga Alhaji Ladan bai yi tambaya ba ko bai kara bayani ba, to kamar bai zo ba ne.

Kasancewarsa a wajen darussan da irin mu’amalarsa ta alheri suna kara jan hankalin wasu mutane zuwa wajen neman ilimi.

MATSAYINSA A KUNGIYAR KULA DA MARASA LAFIYA

Marigayi Alhaji Ladan Wapa ya kasance Mataimakin Shugaban Katsina Hospital Friends Association, karkashin jagorancin Khadimul Islam Alhaji Bilya Sanda.

A wannan matsayi da kuma a matsayinsa na mutum mai son taimakon al’umma, ya kasance yana kokarin ganin an tallafa wa marasa lafiya da masu bukata.

WASU DAGA CIKIN AYYUKAN ALHERINSA

Daga cikin abubuwan da na sani game da irin ayyukan alherin da Marigayi Alhaji Ladan Wapa yake yi akwai:

  1. Biyan kudin magani da asibiti: Ya kasance yana taimaka wa marasa lafiya wajen biyan kudin magani da kudaden asibiti, musamman wadanda ba su da karfin daukar nauyin kansu.
  2. Rabon ruwan sha a Babban Asibitin Katsina: Kullum ana raba ruwan sha a Babban Asibitin Katsina da taimakonsa, wannan aiki ne da mutane da dama suke cin gajiyarsa.
  3. Taimakon mata da suka karbi musulunci : Wasu daga cikin matan da suka karbi musulunci idan suka samu mazajen aure, yana taimaka musu da kayan aure da sauran abubuwan da suke bukata.
  4. Tallafawa mata da jari a kowane wata: Tsawon shekaru, duk wata yana ba mata goma jari domin su samu abin dogaro da kansu da iyalansu.
  5. Taimakon wadanda gobara ko ambaliya ta shafa: Idan gobara ta kone wa mutum gida ko wata annoba ta lalata masa muhalli, yana taimakawa. A wasu lokuta har ana tsara yadda za a sake gyara ko gina gidan.
  6. Biyan kudin haya: Wasu daga cikin masu bukata yana daukar nauyin kudin hayarsu domin kada su kasance cikin matsananciyar wahala.
  7. Samar da gidaje ga masu bukata: Yana da gidaje da yake ba wasu mutane su zauna a ciki tare da iyalansu ba tare da sun biya haya ba.
  8. Daukar nauyin karatun marayu: Ya kasance yana daukar nauyin wasu marayu a makaranta tun daga matakin firamare har zuwa jami’a.
  9. Ciyar da mutane kullum
  10. Daukar nauyin wasu Malaman Addini domin su karantar , a ciki akwai Tafsir da ake gabatarwa tsawon shekaru a Masallacin kusa da shagonsa wanda har gidan Radio ya biya ana sanyawa, sannan duk Idan an gama Tafsir akwai alheri da yake yi wa wasu daga mahalarta.

A gidan Marigayi Alhaji Ladan Wapa, kullum ana girka abinci mai yawa, sannan a raba wa mutanen da suke zuwa domin cin abinci.

Wannan ba wani abu ne da ake yi lokaci-lokaci kawai ba; aiki ne da ya dade yana gudana, kuma mutane da dama sun kasance suna cin gajiyarsa.

GIDAN GAJIYAYYU DA MARAYU: Wani babban aikin da Marigayi Alhaji Ladan Wapa ya yi shi ne ginawa da kula da wani gida da ake daukar gajiyayyu da marayu tsawon shekaru.

Gidan yana da ruwa da wutar lantarki, kuma ana samar musu da abinci sau uku a rana.

Idan ni ko wasu daga cikinmu muka samu baki ko wasu mutane da suka karbi Musulunci, idan muka sanarda Malam Ashafa, sai ya ce:

“Ku kai su gidan bakin Alhaji Ladan Wapa.”

Gidan yana kusa da gidansa. Idan yana tafiya shagonsa, yakan shiga gidan, ya gaishe da mutanen da suke ciki, ya duba halin da suke ciki, ya tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda ya kamata.

Daga baya ya mika kula da wannan gida ga Karamar Hukumar Katsina.

Wannan yana nuna irin yadda yake kallon taimakon gajiyayyu da marasa karfi a matsayin nauyi da ya rataya a wuyansa.

MAI BUKATAR TAIMAKO BA YA WAHALA A GABANSA: A kusa da gidansa kullum akwai mutane da yake ciyarwa da tallafawa. Wasu daga cikinsu har albashinsu yana daukar nauyinsa.

Idan aka kawo masa bukatar taimako daga masallaci, makarantar Islamiyya, wajen wa’azi, Mauludi, marasa lafiya ko wasu masu bukata, ba ya yawan wahalar da mutum da tambayoyi masu yawa.

Idan yana da ikon taimakawa, sai ya taimaka. Idan kuma ba shi da ikon yin hakan, sai ya fada a fili.

Wannan shi ne abin da ya sa mutane da dama suka samu damar zuwa wajensa ba tare da tsoro ko jin kunya ba.

GUDUMMAWARSA GA AIKIN ATTA’AWUN ISLAMIC FOUNDATION: A kwanakin baya, Malaminmu Dr. Ahmad Musa Abdullahi ya ce a gayyaci Marigayi Alhaji Ladan Wapa lokacin da ake bude gidajen marayu da ‘yan gudun hijira na Atta’awun Islamic Foundation.

Mun kai masa katin gayyata, amma ba a samu damar ba shi cikin lokaci ba. Duk da haka, Marigayi ya zo.

Abin mamaki shi ne, bai ma san hakikanin abin da za a yi ba. Abinda ya ji kawai shine ana bude wani gida ne na marayu, sai ya zo.

Da ya iso, ba tare da dogon bayani ko bincike ba, nan take ya bada gudummawarsa.

Wannan karamin labari ne, amma a wurina yana bayyana babban halinsa: idan ya ji ana neman taimakon marayu ko masu bukata, zuciyarsa tana son ya kasance cikin masu taimakawa.

Ayyukan Atta’awun Islamic Foundation na tallafawa marayu da masu bukata, ciki har da samar da gidaje da wasu muhimman bukatu, sun kuma samu kulawa a manyan ayyukan gidauniyar a Katsina.

SHAIDAR MAKWABTAKA DA AL’UMMA: Mutanen da suke zaune kusa da gidan Marigayi sun shaida irin yadda yake ciyar da mutane da taimaka musu.

Ba wai taimakon da ake yi a gaban jama’a kadai ba ne. Akwai abubuwa da dama da mutane ba su sani ba, domin wasu daga cikin ayyukan nasa yana yin su ne ba tare da neman a yaba masa ba.

Ya kasance yana taimaka wa matasa, sabbin musulmai, mata, marasa lafiya, marayu da sauran masu bukata.

ALHERIN DA YA BARI A BAYANSA: Idan aka dubi rayuwar Marigayi Alhaji Ladan Wapa, za a fahimci cewa dukiya a wurinsa ba wai abin tara kudi kawai ba ne. Ya fahimci cewa dukiya wata dama ce ta taimakon bayin Allah.

*Ya taimaka wa mutane da yawa a lokacin da suke cikin bukata.

*Ya ciyar da masu yunwa.

*Ya taimaka wa marasa lafiya.

*Ya tallafa wa mata da jari.

*Ya taimaka wa marayu.

*Ya samar da muhalli ga gajiyayyu.

*Ya tallafa wa sabbin musulmai.

*Ya kuma kasance yana tallafawa ayyukan addini da na al’umma.

Saboda haka, abin da ya bari a baya ba gidaje da dukiya kadai ba ne. Ya bar tarihin mutane da dama da suka samu sauki saboda taimakonsa.

Rayuwar Marigayi Alhaji Ladan Wapa tana koya mana cewa mutum zai iya yin tasiri mai girma a cikin al’umma ba tare da ya rike babban mukamin gwamnati ba.

Abin da yake bukata shi ne zuciya mai tausayi, hannu mai bayarwa da kuma niyyar neman yardar Allah.

Ayyukan alherin da ya yi za su ci gaba da zama shaida a kansa, musamman a zukatan wadanda suka taba cin gajiyar taimakonsa.

Allah Ya gafarta wa Marigayi Alhaji Ladan Wapa, Ya jikansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya yafe masa kura-kuransa, Ya karbi ayyukan alherinsa, Ya sanya su zama Sadaqatul Jariya a gare shi, Ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi.

Allah Ya mayar da irin wannan hali na taimakon al’umma abin koyi ga masu hannu da shuni, domin dukiyar da aka yi amfani da ita wajen taimakon bayin Allah ita ce dukiyar da ta fi amfani ga mutum a duniya da lahira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *