Daga Wakilinmu
Dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Sanata Sabo Mohammed Nakudu ya bayyana takararsa ta shekarar 2027 a matsayin wata manufa ta ceto jihar, da nufin gyara matsalolin shugabanci, inganta tafiyar da gwamnati da rage tsananin matsin tattalin arzikin da al’ummar jihar ke fuskanta.
Nakudu ya bayyana haka ne ranar Lahadi a Dutse, yayin da yake karbar wata tawaga ta Alarammomi da Malaman Tsangaya daga sassan jihar, karkashin jagorancin Goni Mallam Ibrahim Mai Bindiga Hadejia.
Ya ce dalilin tsayawarsa takarar shi ne bukatar sake fasalin tsarin shugabanci, inganta rayuwar al’umma da dawo da amincewar jama’a ga gwamnati.
Sanata Nakudu ya yi alkawarin gudanar da budaddiyar gwamnati, gaskiya da rikon amana, inda bukatu da koke-koken jama’a za su kasance ginshikin tsara manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Ya gode wa tawagar bisa goyon bayansu, tare da alkawarin kara hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a harkar ilimin addinin Musulunci, domin inganta walwala da ci gaban al’umma.
Da yake magana a madadin tawagar, Goni Mai Bindiga Hadejia ya ce sun ziyarci Sanata Nakudu ne domin bayyana goyon baya da mubaya’arsu ga takararsa, bisa la’akari da manufofinsa da ajandar ci gaban jihar.
Shi ma da yake jawabi, Hon. Ado Sani Kiri, tsohon shugaban farko na APC a Jihar Jigawa kuma babban mai ruwa da tsaki a ADC, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar za ta samu nasara a zaben 2027.
Ya bukaci Alarammomi da Malaman Tsangaya da su ci gaba da addu’a da gangamin wayar da kan jama’a domin samun nasarar ADC da ‘yan takararta a dukkan matakan zabe.
