Malamai da Limamai 3,000 Sun Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Na samun Zaman Lafiya Da Nasarar Tinubu

Daga Hussaini Yero,Gusau

Kimanin Limamai da Malamai 3,000 ne daga sassa daban-daban na Jihar Zamfara suka gudanar da addu’o’i na musamman. akan samun dawammamen zaman lafiya da samun nasarar Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunubu a zabe mai zuwa.

An gudanar da addu’oin zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da ƙasar baki ɗaya, a gidan Darakta Janar na yakin kamfen din Shugaban Kasa, Sanata Abdul’aziz Yari, tare da gudanar da zaɓen 2027 mai zuwa cikin lumana ba tare da rikici ba.

Addu’ar ta maida hankali ne kan sojojin Najeriya da sauran jami’an hukumomin tsaro da ke yaki da rashin tsaro, domin Allah ya kare su tare da basu ƙarfi kan dukkannin ‘yan ta’adda da ke hana zaman lafiya a ƙasar.

Daga cikin manyan Limamai da suka yi addu’a akwai Sheikh Liman Dan Alhaji daga babban masallacin Gusau. Ya yi addu’ar akan zaɓen 2027 mai zuwa ya gudana cikin lumana, sannan ya roƙi Allah da ya ba shi ƙarin ƙarfi don fatattakar dukkannin wakilan shaiɗan da ke shirin haddasa rikicin siyasa da na addini a matsayin makami na rushe zaman lafiya a lokacin zaɓen 2027 mai zuwa.

Haka kuma, wani mashahurin Malamin, Sheikh Sadiqu Saddeeq, ya yi addu’ar Allah ya ba Sanata Yari damar gudanar da aikin da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi na kamfen din dawowarsa karo na biyu a mulkin Najeriya.

Sheikh Sadeeq ya ƙara da cewa ya kamata dukannin al’umma masu kishin Jihar Zamfara su sani cewa aikin da aka ba Sanata Yari babban ƙalubale ne ba kawai gare shi ba, har ma ga dukannin al’umma masu kishin jihar.

A nasa jawabin Sanata Yari ya roƙi malamai da manyan limamai da su ci gaba da fadakar da al’umma a Masallatan Juma’a akan kokarin da gwamnatin tarayya keyi akan magance matsalar tsaro, “dan yanzu haka akwai gagarumin shiri da gwamnatin tarayya keyi na daukar sojoji wadanda za suyi aiki a Jihar da suka fito dan magance matsalar tsaron cikin gaggawa”. In ji Sanata Yari.

Sanata Yari ya tabbatar da karin kayan aikin ga jami’an tsaro a cikin Jihar zamfara da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *