Daga Wakilinmu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙaddamar da ginin sabuwar fadar Sarkin Dutse wadda za ta lakume kudi kusan Naira biliyan 2.6.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, wanda ya wakilci Gwamna Umar Namadi wajen aza harsashin ginin, ya ce gwamnati za ta samar da dukkanin tallafin da ake buƙata domin kammala aikin cikin watanni 18.
Ya ce ginin fadar wani muhimmin aiki ne da zai ƙara wa Dutse daraja, tare da cika alƙawarin da Gwamna Namadi, ya yi wa Sarkin Dutse da al’ummar masarautar.
Bala ya buƙaci kamfanin da ya samu kwangilar aikin da ya bi jadawalin da aka tsara domin kammala ginin a kan lokacin da aka kayyade.
Da yake jawabi, Sarkin Dutse, Alhaji Muhammad Hameem Nuhu Sunusi, ya ce ya shafe kusan shekaru 30 yana jiran a gina wa Dutse sabuwar fada ta zamani.
Sarkin ya ce sabuwar fadar ba ta masarautar Dutse kaɗai ba ce, domin za ta zama abin alfahari ga ɗaukacin al’ummar Jigawa.
Ya kuma bayyana cewa tsohuwar fadar Dutse za ta ci gaba da kasancewa wajen karbar baƙi, saboda muhimmancinta wajen adana tarihin da al’adun masarautar.
Shi ma wakilin kamfanin Newpro Quants Consultant (NQC) Limited, Injiniya Abubakar Kaila, ya tabbatar da cewa kamfanin zai kammala aikin a kan lokaci.
Ya ce gwamnati ta riga ta ba su kuɗin fara aikin kuma an fara gudanar da shi.
