Daga Muhd D. Haidar
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta bai wa iyalai da magadan jami’an ’yan sanda 25 da suka rasu yayin da suke bakin aiki, jimillar Naira miliyan 25,960,848.75.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa, CP Tijjani Murtala, ne ya gabatar da cakin a madadin Babban Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, a hedikwatar rundunar da ke Dutse.
Kuɗaɗen na ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da na hatsarin aiki na jami’an ’yan sanda.
CP Tijjani Murtala ya ce tallafin ba zai iya maye gurbin rayukan jami’an da suka rasu ba, sai dai yana nuna kulawa da goyon bayan Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ga iyalan waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen yi wa ƙasa hidima.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kula da jin daɗin iyalan jami’an da suka rasu gwargwadon tanadin tsare-tsaren jin daɗin jami’ai.
A nasa jawabin, wakilin iyalan, Yusuf Muhd. Tsoho, ya gode wa shugabannin ’yan sanda bisa tallafin, yana mai cewa hakan ya nuna kulawar hukuma ga iyalan jami’an da suka rasa rayukansu suna bakin aiki.
An kammala taron da addu’o’in neman rahama ga jami’an da suka rasu da kuma ƙarfi ga iyalansu.
