Daga Wakilinmu
Shugaban Hukumar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Saidu Yahaya, ya yi murabus daga mukaminsa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Rahotannin sun ce murabus ɗin na zuwa ne bayan zargin fuskantar matsin lamba daga gwamnatin jihar, sakamakon damuwa da ake da ita kan alakar siyasa da kuma kusancinsa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sai dai har zuwa yanzu, Saidu Yahaya da gwamnatin Jihar Kano ba su tabbatar da rahoton murabus ɗin ba, yayin da kuma ba a bayyana a hukumance dalilin da ya sa ya ajiye mukamin ba.
Mahangar Arewa ta ruwaito cewar, an nada Saidu Yahaya a matsayin shugaban PCACC a watan Agustan 2025, bayan kammala wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado.
Daga bisani, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da nadin Saidu Yahaya na wa’adin shekaru biyar.
Rahoton murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Jihar Kano, musamman bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Ana sa ran hukumomin da abin ya shafa za su yi karin bayani domin tabbatar da matsayin Saidu Yahaya da kuma dalilin da ya sa aka samu rahoton murabus ɗinsa.
A wata sanarwa, gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Sakatariyar Hukumar Hafsat Adda’u Kutama a matsayin shugaban riko ta wucin gadi.
