Daga Muhd D Haidar
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince fa naɗin Barista Hafsat Ada’u Kutama a matsayin Shugabar Riƙon Ƙwarya ta Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC).
Naɗin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin murabus ɗin shugaban hukumar, Saidu Yahaya, wanda rahotanni suka ce ya miƙa wasiƙar murabus ɗinsa a ranar Talata, 15 ga Satumba, 2026.
Rahotannin sun bayyana cewa murabus ɗin Saidu Yahaya ya biyo bayan wasu matsaloli da ake cewa sun taso tsakanin sa da gwamnatin jihar dangane da yadda yake gudanar da ayyukan hukumar.
Sai dai, ya zuwa yanzu, ba a bayyana cikakkun bayanai a hukumance kan dalilan murabus ɗin ba, don haka bai dace a ɗauki zarge-zargen da ake yadawa a matsayin tabbataccen dalili ba.
Mahangar Arewa ta ruwaito cewar, Saidu Yahaya ya karɓi shugabancin PCACC ne a watan Agustan 2025, bayan kammala wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.
A lokacin da aka kafa sabon tsarin shugabancin hukumar, gwamnatin Jihar Kano ta kuma naɗa Barista Hafsat Ada’u Kutama a matsayin Sakatariya kuma Mai Ba da Shawarar Shari’a ta hukumar.
Da sabon naɗin, Hafsat Kutama za ta jagoranci hukumar a matsayin Shugabar Riƙon Ƙwarya, har zuwa lokacin da za a ɗauki matakin da ya dace wajen cike gurbin shugaban hukumar na dindindin.
Hukumar PCACC na daga cikin muhimman hukumomin da ke da alhakin karɓar tare da binciken korafe-korafe da suka shafi zargin cin hanci da rashawa da sauran abubuwan da suka shafi rashin gaskiya wajen gudanar da ayyukan gwamnati a Jihar Kano.
Masu bibiyar al’amuran jihar na sa ido kan matakin da gwamnatin Kano za ta ɗauka nan gaba dangane da cike gurbin shugabancin hukumar na dindindin, da kuma yadda sabon shugabancin riƙon ƙwarya zai gudanar da ayyukan hukumar.
