Daga Hussaini Yero, Gusau
Dan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro a jihar idan aka zaɓe shi a matsayin gwamna idan kuma ya shekara biyu bai yi abinda ya dace ba akan tsaro zan yi murabus daga mukamin gwamna.
Sanata Marafa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, jim kaɗan bayan ya gana da kungiyoyi daban-daban a wani ɓangare na ayyukan yaƙin neman zaɓensa.
Ya ce matakinsa na tsayawa takarar gwamna ya samo asali ne daga sha’awarsa ta bayar da gudunmawa wajen dawo da zaman lafiya da ci gaba a jihar.
Ya ce yana da gogewa da ƙarfin da zai bayar da shugabanci da zai magance ƙalubalen da jihar ke fuskanta, musamman rashin tsaro.
Game da dabarun da ya tsara na magance rashin tsaro, Sanata Marafa ya ce ba za a iya bayyana cikakkun bayanai na ayyukan da zai wa al’ummar Jihar ba sai randa aka rantsar dashi a matsayin gwamna sannnan zai bayyana.
Ya tabbatar da cewa, idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fara aiki tuƙuru bayan lokacin mika mulki, tare da cikakken shirin tsaro da za a aiwatar tun daga farko.
Sanata Marafa ya ce zai ba kansa shekara biyu don cimma matsalar tsaro da ke cikin ikon gwamnatin jiha, yayin da yake sa ran Gwamnatin Tarayya za ta magance na ta nauyin.
Ya yi alkawarin cewa, a cikin shekaru biyu, idan gwamnatinsa ta kasa cimma aƙalla kashi saba’in da biyar cikin ɗari na manufofinta na tsaro, zai yi murabus daga mukaminsa.
Dan takarar gwamnan ya bayyana cewa zai kaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓe da za su kwashe kwanaki biyar da aka tsara don tuntuɓar masu ruwa da tsaki, gudanar da tarurruka da kuma tuntuɓar mazauna yankin kan batutuwan da suka shafi jihar.
A cewarsa, tattaunawar na da nufin tantance matakin karɓuwar jam’iyyar, gano wuraren da ke buƙatar ƙarin kulawa da ƙarfafa tsarin yaƙin neman zaɓenta kafin zaɓe.
