Shinkafi Ya Zargi INEC Da Yin Watsi Da Umarnin Kotu Kan Tikitin APC Na Sanatan Zamfara ta Arewa

Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna

Wani jigo a jam’iyyar APC, kuma ɗan takarar kujerar Sanata mai wakiltar Zamfara ta Arewa, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, kan abin da ta bayyana a matsayin wallafa sunan Sanata Sahabi Alhaji Ya’u a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC na Zamfara ta Arewa ba bisa ƙa’ida ba.

Shinkafi bayana hakan a wata wasiƙa a ranar 18 ga Satumba, 2026, yayin da INEC ta wallafa sunan Ya’u duk da cewa akwai hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, wanda ya soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani.

Mai shari’a Hassan Dikko na Babbar Kotun Tarayya, da ke Gusau, ne ya yanke hukuncin a ranar 31 ga Agusta, 2026, a cikin ƙarar da ke da lamba FHC/GS/CS/6/2026.

Kotun ta soke zaɓen fidda gwani da aka ce an gudanar a ranar 19 ga Mayu, 2026, tana mai cewa an gudanar da shi ne ta hanyar da ta saɓa wa tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026, da kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC da kuma ƙa’idojin jam’iyyar.

Musamman, kotun ta umarci jam’iyyar APC da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin dukkan ‘yan takarar da aka tantance, cikin kwanaki 14 daga ranar da aka yanke hukuncin.

Kotun ta kuma umarci hukumar Zaben da ta amince tare da wallafa sunan duk wanda ya samu tikitin jam’iyyar ta hanyar sabon zaɓen fidda gwanin da aka gudanar bisa ƙa’ida.

Ta hannun lauyoyinsa, Shinkafi ya rubuta wa Shugaban INEC wasiƙa a hedikwatar hukumar da ke Abuja, yana neman a gaggauta cire sunan Ya’u daga cikin jerin sunayen ‘yan takarar da hukumar ta wallafa.

A cikin wasiƙar da lauyan mai suna S.Y. Aliyu ya sanya wa hannu, lauyoyin sun ce wallafa sunan wani ɗan takara kafin gudanar da sabon zaɓen fidda gwani, ko kuma kafin a kammala dukkan matakan ɗaukaka ƙara, na raunana ikon bangaren shari’a tare da saɓa wa ƙa’idoji da dokokin zaɓe.

Shinkafi ya bayyana matakin da INEC ta ɗauka a matsayin wanda bai dace ba kuma babu adalci, yana mai cewa hakan na iya yin illa ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ya ce INEC, a matsayinta na hukumar da ke kula da zaɓuka, ba za ta iya yin watsi da umarnin kotun da ke da hurumin shari’a ba.

Shinkafi ya kuma tuna cewa a wasu zaɓukan da suka gabata, Kotun Ƙoli ta soke wasu zaɓukan fidda gwanin jam’iyyar APC saboda rashin bin ƙa’idoji, inda aka ba wasu jam’iyyu da suka zo na biyu nasara, ciki har da wasu zaɓukan gwamnonin jihohi.

Wasiƙar ta ce ya kamata INEC ta kare sahihanci da amincin tsarin zaɓe, ciki har da yadda jam’iyyun siyasa ke gudanar da zaɓen fidda gwanayensu.

Sanarwar dokan ta lissafa wasu umarni takwas da kotun ta bayar, ciki har da umarnin hana jam’iyyar APC, INEC da Sanata Ya’u ci gaba da aikata abin da zai saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da dokokin ƙasa.

Kotun ta kuma bayyana cewa matakan da jam’iyyar APC da Ya’u suka ɗauka ba su yi daidai da kundin tsarin jam’iyyar ba, tare da cewa ba a bi tsarin da ya dace ba wajen gudanar da zaɓen fidda gwanin ranar 19 ga Mayu.

Lauyoyin Shinkafi ta haɗa kwafin hukuncin kotun da aka tabbatar da sahihancinsa, da kuma kwafin sanarwar da INEC ta wallafa, cikin wasiƙar da aka aika wa hukumar.

Sun kuma buƙaci hukumar da ta dakatar da duk wani mataki dangane da wannan batu, har sai an gudanar da sabon zaɓen fidda gwani ko kuma an kammala hukuncin duk wata ƙara da aka ɗaukaka zuwa babbar kotu.

Yayin da wa’adin kwanaki 14 da kotun ta bayar na gudanar da sabon zaɓen fidda gwani ya fara daga ranar 31 ga Agusta, lauyan Shinkafi ya ce abin da ya kamata a yi a yanzu shi ne jam’iyyar APC ta gudanar da zaɓen da kotu ta umarta, sannan INEC ta yi aiki da sakamakon zaɓen.

Wannan ci gaba ya ƙara jawo ce-ce-ku-ce a Zamfara ta Arewa, inda wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka rabu kan sahihancin zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a watan Mayu da kuma wanda ya kamata ya kasance ɗan takarar jam’iyyar.

Shinkafi, wanda shi ma ɗan takara ne na kujerar, ya ce zai ci gaba da bin tsarin da doka ta tanada, tare da ƙoƙarin bin doka da oda a cikin jam’iyyar APC.

Ya yi kira ga INEC da ta gaggauta janye sunan da aka wallafa a halin yanzu, domin kauce wa yiwuwar zargin raina umarnin kotu, tare da kare amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *