Daga Abubakar Rabilu Gombe
Shugaban ƙungiyar Arewar Mu Duniyar Mu African Chiefdom and Council, kuma Sarkin Hausawan Tukulma a Jihar Gombe, Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan mutuwar mutane 37 da suka mutu yayin da suke tsare a hannun jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja.
Ambasada Ibrahim ya ce lamarin ya haifar da damuwa, yana mai cewa ya zama wajibi a gano ainihin abin da ya faru da kuma musabbabin mutuwar mutanen, waɗanda aka ce an kama su ne bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, rahotannin farko sun nuna cewa mutane 33 ne suka mutu, kafin daga bisani adadin ya ƙaru zuwa 37. Ya ce ya kamata binciken ya kasance mai zaman kansa, na gaskiya kuma cikin gaggawa, domin tabbatar da yadda mutanen suka mutu da kuma tantance ko an samu wani sakaci ko take haƙƙinsu yayin da suke tsare.
“Wannan kira ba na zargi ba ne, kuma ba na tayar da hankali ba ne. Kira ne na adalci, gaskiya, bin doka da kare rayukan al’umma,” in ji shi.
Sarkin Hausawan Tukulma ya buƙaci binciken ya duba yanayin wuraren da ake tsare da mutanen, tsawon lokacin da suka yi a tsare, irin kulawar da aka ba su, da kuma ko sun samu isasshen abinci, iska da kulawar lafiya.
Ya kuma buƙaci a gudanar da cikakken binciken likitanci da na forensic domin gano ainihin musabbabin mutuwar kowanne daga cikin waɗanda suka rasu, ya kara da ce bai kamata a yi gaggawar yanke hukunci kan lamarin ba kafin a kammala binciken kwararru da samun cikakkun bayanai.
Kiran na Ambasada Ibrahim ya zo ne a daidai lokacin da ake gudanar da bincike kan lamarin, bayan hukumomin Jihar Neja sun ɗauki matakan da suka dace domin gano abin da ya faru, ya yi kira da a bai wa iyalan waɗanda suka mutu cikakken bayani kan halin da ’yan uwansu suka shiga kafin mutuwarsu da kuma sakamakon binciken da hukumomi za su gudanar.
A cewarsa, idan bincike ya gano cewa wani jami’i ko wata hukuma ta karya doka ko ta take haƙƙin waɗanda ake tsare da su, ya kamata a ɗauki matakin da ya dace bisa tanadin doka, ya ƙara kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa matakan kare haƙƙin waɗanda ake tsare da su, tare da tabbatar da cewa irin wannan lamari ba ya sake faruwa a nan gaba.
Haka kuma, ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu, sannan su bai wa hukumomin da suka dace damar gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci, ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya bai wa iyalansu haƙuri, Ya kuma tabbatar da adalci da zaman lafiya a Jihar Neja da Najeriya baki ɗaya.
