Cikar Jihar Zamfara Shekaru 30: Al’umma Sun Amfana Da Ayyukan More Rayuwa…Nakwanda

Daga Hussaini Yero,Gusau

A Gobe ne, 1 ga Oktoba 2026, Jihar Zamfara za ta cika shekara 30 da samuwa. Shekaru talatin al’umma sun amfana da ayyukan more rayuwa ta kowane bangare.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Nakwada ne ya bayyana haka a taron manema labarai a ofishinsa da ke sakatariyar Jibril Bala Yakubu da ke Gusau.

Nakwada ya bayyana cewa,tarihin shekaru 30 da samuwar jihar Zamfara abun godiya ne ga Allah da kuma murna ga al’umma, sarakunan gargajiya, ma’aikatan gwamnati da ‘yan ƙasa waɗanda suka bayar da gudummawa wajen ci gaban Zamfara tun lokacin da aka kirkiro ta a shekarar 1996.

“Muna godiya ga waɗanda suka bada gudummawa tare da girmamawa da sadaukarwar da kai ds su kayi wajen samuwar Jiharmu ta Zamfara.

“A lokaci guda, wannan bikin cika shekaru yana nazari kan sauyi da aka samu a cikin shekaru uku da suka gabata ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, na Jihar Zamfara, da kuma shiga sabon babi a tafiyar ci gabanmu na shekaru 30.

Tun daga watan Mayu 2023, gwamnatin ta samu ci gaba a fannonin tsaro, ilimi, kiwon lafiya, noma da ababen more rayuwa, ci gaban ɗan adam, gyaran cibiyoyi da ci gaban tattalin arziki.

“Gwamnatin ta tabbatar da cewa ba za a iya samun sauyi mai ma’ana da ɗorewa ba tare da tsaro ba.

” A Jihar da ta sha fama da harin ‘Yan bindiga, garkuwa da mutane da tarwatsa rayuwar mutanan karkara.dawo da tsaro ya zama ginshiƙi wajen sake gina al’ummomi, da dawo da su garuruwan su ,su ci gaba da noma dan shine ginshikin tattalin arzikin su”.

Nakwada ya tabbatar da cewa, gwamnatin Jihar ta ci gaba da bayar da gagarumin goyon baya ga rundunar Sojoji, da ‘Yan Sanda ta Najeriya, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Hukumar Tsaron Farar Hula da sauran hukumomin tsaro na yau da kullum da ke aiki a Zamfara.

“Mun samar da motocin aiki, motocin yaƙi masu sulke, jiragen sama marasa matuki na leƙen asiri (drones), babura na musamman da sauran kayan aiki na dabaru da aiki domin ƙarfafa motsi, sa ido, tattara bayanan sirri da kuma gaggauta kai dauki”.

A matakin jiha Gwamnati ta kafa Ƙungiyar Tsaron Al’umma (Community Protection Guards – CPG) a matsayin ƙungiyar tsaro mai goyon bayan Jihar domin tallafawa hukumomin tsaro na yau da kullum, musamman ta fuskar bayanan sirri dan dakile ‘yan bindiga da suka addabe mu.

A cikin bukukuwan cika shekaru 30 da samun Jiha gobe , za’a kaddamar da fara jigilar matafiya a filin jirgin sama da gwamnatin Jihar ta gina da kuma kaddamar da ayyukan da Gwamna Dauda Lawal yayi da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *