Daga Muazu Hardawa Bauchi
Wata matar aure mai suna Jamila Adamu Tatimu mai shekara 43 ta gamu da ajali ta rasa ranta a Bauchi, sakamakon fashin kabewa da tabarya da ake zargin amaryar ta, da yi mata saboda dalili irin na kishi.
Al’amarin ya faru ne a rukunin gidajen Tafawa Balewa da ke Bauchi, yadda bayanan da muka samu ya nuna cewa, matar da ake zargi ta kai wa marigayiyar harï da tabarya, lamarin da ya yi sanadin mutüwar ta nan take saboda yadda bugun ya sa kwakwalwarta ta zubo waje.
Bayan faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi SP Nafiu Habib ya ce lamarin ya faru a yammacin Ranar lahadi 28/9/2026.
Ya ce jami’an tsaron ‘yan sanda na rukunin gidaje sun samu rahoton kishiyar mai suna Hauwa Haruna mai shekara 33 ta kashe kishiyar ta da tabarya da misalin karfe hudu na yamma.
Inda ‘yan sanda suka kama matar da ake zargi, a halin yanzu tana hannun su domin ci gaba da gudanar da bincike a sashen manyan laifuka na SCID. A lokacin da kakakin rundunar SP Nafiu Habib ya zanta da Hauwa Haruna ta bayyana cewa ta yi mafarki ne kishiyar ta zo a matsayin kyanwa za ta kashe ta, shine zuciya ta raya mata daukar matakin gaggawa kafin ta kashe ta, don haka ta riga daukar matakin.
Ta kara da cewa tana aikata matakin ta goyi tagwayenta namiji a baya macen a hannu ta tafi gidan babanta, yadda ta bayyana abin da ta aikata da cewa ta yi riga Malam masallaci ne amma ta yi nadama ta san za a zo a kamata. Don haka tana jiran ita ma a zartas mata da hukuncin kisa.
Amma wata majiya mai tushe daga dangin marigayiyar sun bayyana mana cewa wannan ba shi ne zargin farko ba kan kishiyar na illata Uwargidan ta amma mijin bai dauki mataki mai zafi ba. Saboda a baya ta sha dukan kishiyar ta zuba mata ruwan zafi ta konata, bayan an sasanta sun sake fada ta karyata sau biyu.
Bayan faruwar lamarin mijin
nasu mai suna Abdullahi Askiya ya kai ta asibiti an ba su takardar shaidar tana da tabin hankali amma an mata jinya ta ji sauki, amma daga baya ta kashe ta.
Iyalan Jamila sun bayyana matuƙar alhini kan rasuwar, tare da yin kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru da tabbatar da an bi mata hakki wajen yin adalci don a yi mata hukunci daidai da laifin ta.
Kakakin ‘Yan sandan SP Nafiu Habib ya ce suna ci gaba da bincike kuma ana daukar matakin ganin an yi mata hukunci har shi mijin da ake ganin ya yi sakaci har lamarin ya munana.
Bayan tabbatar da rasuwar ta a asibitin kwararru na Bauchi, an gudanar da jana’izar Jamila Ranar litinin, yayin da Hauwa’u take hannun ’yan sanda a sashen binciken manyan laifuka.
Mai Martaba Sarkin Bununu a jihar Bauchi Alhaji Jibrin Danlami Hassan wanda ke cikin dangin marigayiyar Jamila cikin jawabinsa ga wakilin mu, ya bayyana cewa ya kamata lamarin ya zama babban darasi kan illar fushi da kishin tsakanin ma’aurata.
Don haka ya ja hankalin magidanta su rika lura da halin da iyalai suke ciki su guji yin sakaci da matsala komai karantar ta, su gaggauta daukar matakin gaggawa da ya dace don yin sasanci tsakanin kishiyoyi, idan an ga matsalar ta tsananta a raba musu gida don samun maslaha.
Alhaji Jibrin Danlami ya yi adduah Allah Ya jiƙan Jamila Adamu da Rahama, Ya gafarta mata, Ya bai wa iyalan ta haƙurin jure wannan babban rashi.
Bayan haka ya gargadi mata masu saurin fushi da zafin kishi, su riƙa kai zuciya nesa a rika hakuri don gujewa nadamar da ba za ta iya gyara abin da ya lalace ba.
Daga karshe ya ja hankalin ofishin Uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Mohammed a karkashin shirin ta na magance cin zarafin jinsi, GBV a shiga cikin lamarin a bi hakkin wacce aka kashe don ganin an hukunta mai laifin gwargwadon laifin ta.
