Daga Wakilinmu
Kwamitin shirye -shiryen musabukar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 41 da za a gudanar a Jihar Jigawa sun kai ziyarar aiki ga fadar mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu.
Da yake jawabi Shugaban kwamitin tsare-tsare, Dr Lawan Inusa Danzomo wanda kuma shine kwamishinan Ilmi a matakin farko ya bayyana cewar sun Kai ziyarar ne domin neman shawarwari da addu’ar samun nasarar taron daga mai martaba Sarki.
Kwamishinan ya kara da cewar Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki kudirin bada ko wanne irin tallafi na ganin musabukar karatun Alkur’ani mai tsaki ta samu gagarumar nasara.
Dr Lawan Danzomo ya kara da cewar a halin yanzu an kafa kananan kwamitoci guda goma dan samun nasarar shirin, ya kara da cewar kwamitocin sun hada da kwamatin gurin zama da karbar baki, kwamitin ciyarwa da zirga-zirga da kuma kwamitin kula da lafiya.
Saurar sun hada dana kula da al’amurran mata, yada labarai, tsaro, bada kyautuka da dai sauransu.
Ana sa jawabin Mai martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussaini Adamu wanda Makaman Kazaure, Alhaji Jamilu Umaru Adamu ya wakilta ya tabbatar da kudirin majalisar mai martaba Sarkin Kazaure kan bada kowacce gudunmawa na ganin musabukar ta samu gagarumar nasara.
Mai girma Makaman Kazaure ya kara da yiwa dukkanin Yan’ uwa Musulmi murnar wannan falala da fa’ida da za ta same mu a Jihar Jigawa.
Alhaji Jamilu yayi addu”a ga mai girma Gwamna Mallam Umar Namadi, kan Allah ya kara bada zaman lafiya a Jihar Jigawa tare da karuwa arziki.
Cikin ‘yan tawagar sun hada da kwamishin ma’aikatar aiyuka, Alhaji Gambo Shu’aibu Malam da kwamishinan ma’aikatar kula da kananan hukumomi, Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa manyan kusoshin gwamnati da dai sauransu.
*GAMBO GARBA AUJARA
