Daga Mati Ali
Dan takarar gwamnan Jihar Jigawa na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Sanata Sabo Mohammed Nakudu ya ce ba a kafa jam’iyyar domin haifar da rarrabuwar kawuna ta fuskar addini, kabila, harshe ko al’ada ba, sai dai domin tabbatar da daidaito da bai wa ’yan Najeriya damar gudanar da addininsu da kiyaye al’adunsu ba tare da wariya ba.
Nakudu ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar ƙungiyoyin Kiristocin ADC a Jihar Jigawa da suka kai masa ziyarar girmamawa a gidansa da ke Dutse.
Ya ce matsin tattalin arzikin da ake fuskanta ya kamata ya sa shugabanni su mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa da adalci, maimakon amfani da bambancin addini, harshe da al’adu wajen cimma muradun siyasa.
Ya kuma ce idan ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya lashe zaɓen 2027, jam’iyyar za ta mayar da hankali wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa tare da tabbatar da adalci da daidaito.
Nakudu ya kuma tabbatar wa Kiristocin Jigawa cewa za su samu dama su taka rawa a harkokin mulkin jihar idan ADC ta samu nasara a zaɓen 2027.
Da yake jawabi, shugaban tawagar, Rev. Musa Alasan Taura, ya ce sun kai ziyarar ne domin tabbatar da goyon bayansu ga ADC, Atiku Abubakar, Nakudu da sauran ’yan takarar jam’iyyar.
Daga cikin ƙungiyoyin da suka kai ziyarar goyon baya daban-daban akwai Birnin Kudu ADC New Movement 2027, ƙungiyar direbobin kasuwanci ’yan ADC, Atiku-Nakudu-Baraya-Bala-Dalhatu Movement da Danmodi Greenlight Association ta Kiyawa, wadda ta sauya suna zuwa Nakudu Greenlight Association.
