An Kaddamar da Sabbin Ayyuka na Samar da Hasken Lantarki mai Amfani da Hasken Rana a Dajin Yankari

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin gwamna Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ta kaddamar da wasu sabbin ayyukan inganta ababen more rayuwa a gandun dajin Yankari Game Reserve da Sumu Wildlife Park, domin bunƙasa yawon buɗe ido da kare namun daji a cikin dazukan.

Mataimakin Gwamnan, Hon. Auwal Muhammad Jatau, ne ya wakilci Gwamnan Bala Mohammed a wajen bikin kaddamar da hasken lantarki na solar, tare da tawagar hukumar kasafta kudin Kasa ta RMAFC.

Ayyukan da aka bude Yankari sun haɗa da samar da lantarkin hasken rana da gyaran tsarin samar da ruwan famfo a dajin da gidaje, yayin da a dajin Sumu aka yi katanga mai fadin kilomita murabba’i 81, aka gina madatsar ruwa da ƙofar shiga ta zamani.

Shugaban hukumar RMAFC, Dr. Mohammed Bello Shehu, ya yaba da yadda gwamnatin Bala Mohammed ta yi amfani da kuɗaɗen Natural Resources Development Fund wajen ayyukan da za su amfani al’umma.

Ana sa ran ayyukan za su ƙara bunƙasa yawon buɗe ido da kare namun daji da samar da guraben inganta tattalin arziki ga al’ummomin kewayen dajin shakatawa na Yankari da karamar hukumar Alkaleri da kewaye.

An kaddamar da aikin samar da hasken lantarki mai amfani da hasken rana a gandun dajin shakatawa na Yankari da ke jihar Bauchi a kan kudi sama da naira Milyan dubu Uku.
Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir shine ya Samar da aikin.

Dr Mohammed Nasir shine shugaban hukumar yawon shakatawa ta jihar Bauchi kuma Mai lura da gandun daji a jihar Bauchi, ya bayyana cewa samar da hasken solar zai taimaka wajen inganta ayyukan gandun dajin na Yankari, saboda za su samu saukin rashin hasken lantarki da sayan man gas wato diesel da ke cinye musu makudan kudi sama da naira Milyan 500 duk shekara, saboda ba sa aikin da hasken lantarki na Kasa.

Don haka Dr Nasir ya bukaci masu sha’awar yawon shakatawa daga ko ina su zo Yankari don ganin baiwar da Allah ya yi wa dajin na dabbobi da ruwan Wikki da albarkatun daji da bishiyoyi da yanayin muhalli irin na manyan kasashen duniya da suka shahara a yawon shakatawa.

Ya kara da bayyana samar da tashar hasken ranar za ta inganta muhalli a gandun dajin Yankari tare da hana dabbobin shiga rudanin karar injinan samar da lantarki da hayakin da ke gurbatad da muhalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *