Gwamnatin Jigawa za ta samar da tashoshin Radiyo FM na al’umma a garuruwa 5

Daga Wakilinmu

Gwamnatin Jihar Jigawa za ta samar da tashoshin Rediyon al’umma na FM a garuruwa 5 da ke Jihar.

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Hon Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartaswa, inda ta amince da ware kudi naira bilyan 1.337 domin aikin gyara babban gidan radiyon na jihar tare da samar da sabbin gidajen radiyon FM na al’umma guda biyar (community F.M stations).

Garuruwan da za a samar da tashoshin radiyon F.M ɗin sun haɗa da Gumel, Gwaram, Hadejia, Kazaure da Ringim.

Kuɗaɗen da aka ware ɗin sun shafi gyararraki, da sayo kayan aiki a babban gidan radiyo na jiha sai kuma sayo manyan na’urorin yada labarai na zamani wadda za a saka a sabbin tashoshin rediyon FM ɗin da za a gina.

Manufar samar da waɗannan tashoshin shi ne sake faɗaɗa harkokin yaɗa labarai da isar da sakonni da wayar da kan al’umma tare da ilimintar da su a kowane lungu da saƙo na wannan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *